SABON SALON DANFARA A NAJERIYA

SABON SALON DANFARA

Hakika zaku yarda da ni cewa yawaitar shafuka a intanet da tallace da tallace a radiyo da yaduwar fama-famai na siyarwa wai duk da niyyar za;a baiwa mutum jari kyauta. Ko kuma ace ya kawo kudi a juya duk sati ko wata kana da kaza da kaza. Sune yanzu suke cin karansu babu babbaka, saboda gafala da mutane suke da ita sai sunyi kudi ko ta halin ka ka.

Da yawa daga cikin irin wadannan shirye-shirye ba na gaskiya ba ne, kuma suna yin kamamceceniya da na gasken. shi ya sa hukumomi da dama suke ankarar da mutane cewa a kula.

HANYOYIN DA ZAKA GANE YAN DANFARA

  1. idan ance ana daukar ma;aikata misali a Custome, Prison, Airforce, N-Power, da sauransu, to ka shiga shafin hukumar kai tsaye, zaka ga tallan idan baka gani ba to karya ne.
  2. idan kuma kungiya ce (NGO) ko Kamfani, to ka fara duba rijistar kamfanin ko kungiyar da RC nambar a shafin C.A.C (Coporate Affairs Commission). Idan sunan da RC nambar da suka bayar ya yi dai-dai da wanda ka gani a shafin C.A.C to na gaske ne, idan bai yi dai-dai ba, sai ka kiyaye. Za Ka iya sacin rijistar kamfani ta wannan shafin. http://publicsearch.cac.gov.ng/comsearch/index.php
  3. Duk wani shirin tallafi na Gwamnati ko na NGO da ke da kulawar hukumomin Kasa da na duniya kamar World Bank, Unicef, WHO ko CBN, BOI, BOA DBN kyauta ne, babu wani abu mai kama da kudin form. Bankin Duniya shima ya barranta kansa da wani shiri da ake karbar kudin form, duba wannan: http://www.worldbank.org/en/news/press-release/2017/09/06/fraud-alert-world-bank-warns-of-co-operative-scheme-scam

Hakama Development Bank of Nigeria (DBN) shima yace ayi hattara; http://devbankng.com/

  1. Coporate email. Yawancin wadannan yan danfara email din da suke amfani da shi baya aiki ko kuma gamagarin email ne. ina nufin akarshen sa zaka ga yana karewa da …yahoo.com ko…..gmail.com ba asalin sunan hukumar ko kungiyar ba. Ga misalan email da ba gamagari ba na hukumomin gwamnati: cservice@cac.gov.ng, info@devbankng.com,

 

  1. Horaswa: duk wata hukuma ta gwamnati ko mai zaman kanta idan zata baka kudi don yin kasuwanci ta na yin horaswa ko ta nemi ka rubuta bayanan kasuwancin da zaka yi (Business Plan).
  2. Lambar Waya: da yawa daga cikin irin wadannan shafuka zaka ji sunce ga lambar wayanan ka kirawo su. Ko kuma su yi maka sakon karta kwana (SMS) suce ka kirawo lambar wayar su.
  3. Ba sa gama sayar da form: Masu irin wannan shafin a ko yaushe tallan form din su suke yi, kuma babu adadin yawan mutanen da ake nema.

Allah ya ganar da mu.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s

%d bloggers like this: